14:00 - 29/07/2018 - Comments : 0More >>
Take laifi
Alkurani yana gargadi ga masu gatse game da mummunar makomarsu, har ila yau yana tsoratar da su game da ...
Alkurani yana gargadi ga masu gatse game da mummunar makomarsu, har ila yau yana tsoratar da su game da mummunan sakamakon wannan aiki nasu. Kamar yadda wannan ayar ke cewa: وَيْلٌ لِّكُلّ‏ِ هُمَزَةٍ لُّمَزَةٍ (هُمَزَةٍ: آیة 1) (١ "Tsananin azaba ya tabbata ga dukan mai nune mai zunde". Kamar kuma yadda Imam Ali (a.s)ya ce: "Duk mai neman aibun mutane to ya fara da kansa." (Littafin Gurarul Hikam shafi na 659_daga littafin kyautata Dabiu na syed Mujtaba Musawi Lari)
 19:57 - 14/07/2018 - Comments : 0More >>
Take laifi
Wajibi ne a kan mutum idan yana so ya yi wa abokin sa nasiha don yin gyara game da aibin sa...
Wajibi ne a kan mutum idan yana so ya yi wa abokin sa nasiha don yin gyara game da aibin sa, kada ya yi garaje, ya biyo mada ta hikima, domin kada ya Kara da cutar da shi ta hanyar cin mutuncin sa ko harzuka zuciyar sa. Wani malamin tarbiya yana cewa: " Zaku Iya fadakar da Wanda kuka so akan kuskuren sa ta hanyar zura masa ido, ko yin wani motsi, ko daga murya (gyaran murya) ba tare da kun yi magana ba. Domin idan kun ce da shi ya yi kuskure ba zaku iya sa ya amince ba kamar yadda kuke tsammani. Saboda ta hangar bayyana kuskuren sa, zai iya yiwuwa ku dagula tunanin sa, kuma ku ta da hankalin sa, a sakamako haka sai ku cutar da shi akan manufar sa da abin da zuciyar sa ta yarjewa, yin hakan zai iya sanya shi ya ja da Ku ba tare da canja raayin sa ba, ko da kuwa kun ambato masa duk kan bayanan hikima domin da Ilimi, saboda kun riga kun bakanta masa abin da shi ne mafi soyuwa, mafi daraja da zama abin kauna a gare shi. Ku kiyayi fara maganar ku da cewa mutum: zan tabbatar maka, zan kawo maka dalilai. Maanar irin wannan magana ita ce Ku ne kuka fi wayo da hankali, Gyara tunanin mutane kuwa abu ne mawuyaci musamman ma idan aka bi ta mahangar da bata dace ba, ko kuma aka samar da wani shamaki na musamman. Idan har kuna son Ku gyara wani abu to lalle ne ku yi shuru da bakin ku, kada ku yaya ta shi ga kowa; Ku ci gaba kawai da abin da kuke son gudanarwa cikin hikima domin kada wani ma ya gane inda kuka dosa. Ku yi aiki da fadar masu hikima cewa : Ku koyar da mutane ba tare da kun zamanto malamin su ba".
 19:25 - 16/06/2018 - Comments : 0More >>
 08:05 - 13/05/2018 - Comments : 0More >>
 20:28 - 12/05/2018 - Comments : 0More >>

2 3 4 5 6 Next Page >>